Gwamnan Kano Abba Kabir ya bayar da motoci 10 ƙirar Hilux da babura 60 ga dakarun tsaron da ke yaƙi da ƴanbindiga a jihar.
Cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce gwamnan ya yaba wa dakarun da ke yaƙi da ƴanbidigar da ke addabar wasu ƙananan hukumomin jihar.
Gwamnan ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da bai wa jami’an tsaro goyon baya wajen yaƙar ayyukan ƴanbindigar a faɗin jihar.
Matakin na zuwa ne a lokacin da Babban Kwamandan Runduna ta ɗaya ta sojojin dake Kaduna, Manjo Janar Abubakar Sadiq Muhammad Wase, ya kai ziyara jihar domin duba dakarun da ke yaƙi da ƴanbidiga a jihar.
A baya-bayan nan an samu rahotonnin ɓullar hare-haren ƴanbidiga a ƙananan hukumomin da ke iyaka da jihar Katsina mai fama da matsalar tsaro.
