
Bashir Ahmad, hadimin Muhammadu Buhari karyata labarin cewa tsohon shugaban kasar na cikin wani mummunan yanayin rashin lafiya a birnin Landan
“Labarin da ke yawo cewa Buhari na fama da mummunar rashin lafiya har yana kwance a ɗakin kulawa na musamman (ICU), ba gaskiya ba ne.
Aminiya ta rawaito cewa tsohon hadimin ya tabbatar da cewa Buhari ya yi rashin lafiya a baya, amma yanzu yana samun kulawar likitoci kamar yadda ya kamata.
“Lamarin ba kamar yadda wasu kafafen labarai ke yaɗa labari suka ruwaito ba, Buhari yana cikin yanayi mai kyau kuma magunguna na aiki a jikinsa,” in ji Bashir.
Ya kuma ƙara da cewa suna fatan zai samu cikakkiyar lafiya nan ba da jimawa ba.
Idan ba manta ba, Garba Shehu, mai magana da yawun Buhari ne, ya bayyana cewar yana cikin mawuyacin hali a birnin Landan.