Kungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta ƙaddamar da wani gangamin wayar da kai na yaƙi da ɗaukar doka a hannu, tare da kiran hukumomi da su tabbatar da adalci wajen hukunta masu laifi.
An ƙaddamar da gangamin ne a birnin Kano, a ranar Laraba, 28 ga Janairun 2026.
Kungiyar ta bayyana damuwa kan yawaitar ɗaukar doka a hannu musamman kan mutanen da ake zargi da laifuka kamar maita, sata, ƙwacen waya da sauran miyagun laifuka.
Da yake ƙarin bayani, Babban Kungiyar na ƙasa, Malam Isa Sanusi, ya ce gangamin na da nufin daƙile irin waɗannan ayyuka da ke janyo salwantar rayukan ‘yan kasa ba tare da bin doka ba.
Malam Sanusi ya jaddada buƙatar hukumomin da su riƙa bin hanyoyin doka wajen gudanar da bincike da hukunta duk wanda aka samu da laifi, domin kare rayuka, tabbatar da adalci, da tabbatar da adalci a cikin al’umma.
