Hukumar Kula da Bunƙasa Kiwon Dabbobi ta Jihar Kano ta yi wa dabbobi sama da miliyan 5.5 allurar rigakafin cututtuka daban-daban a cikin shekaru uku da suka gabata.
Jami’in aikin, Ibrahim Garba Muhammad, ya ce babu wata jiha da ta kai Kano wajen yin irin wannan babban aikin rigakafin dabbobi.
Ya ce an kuma zuba sama da naira biliyan ɗaya wajen horas da Fulani makiyaya da bunƙasa samar da Madarar Shanu.
Hukumar ta samar da asibitocin dabbobi, cibiyoyin karɓar madara kusan 98, da kuma wuraren adana madara da za su samar da lita miliyan 15 a shekara.
Aikin bunƙasa kiwon dabbobin, wanda Bankin IsDB ya tallafa da dala miliyan 95, ya taimaka wajen ƙarfafa tattalin arziki da samar da ayyukan yi a Jihar Kano.
