Ministan harkokin wajen Masar ya ce da gangan Isra’ila ke kai hari kan Falasɗinawa da ke zuwa karɓar agaji a zirin Gaza.
Badr Abdel-Atty ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai wata ziyara a iyakar Rafah da Gaza tare da Firaministan Falasɗinawa.
Firaminista Muhammad Mustafa ya ce akwai buƙatar ƙasashen duniya su ƙara matsa lamba kan isra’ila ta bayar da damar shigar da ƙarin agaji Gaza.
Wakiliyar BBC ta ce Isra’ila na musanta zargin da ƙungiyoyin agaji fiye da 100 suka yi na cewa tana hana su shigar da agaji da gan gan, inda ta ɗaura laifin kan ƙungiyoyin da kuma Hamas.
