Najeriya ta magantu kan saukar gaggawar da jirgin kasar ya yi a Burkina Faso.
A wata sanarwar da rundunar Sojin saman kasar nan ta fitar ta ce, jirgin ya taso daga Legas ne zuwa kasar Potugal amma wata matsala ta sa yayi saukar gaggawa.
“Ma’aikatan rundunar soja saman na cikin ƙoshin lafiya kuma sun samu kyakkyawar kulawa daga hukumomin da suka karɓi baƙuncinsu”.
Sanarwar ta ci gaba da cewa saukar jirgin a Burkina Faso ba laifi bane domin sauka a filin jirgin sama mafi kusa, idan matsala ta faru na cikin ƙa’idojin tsaro da ka’idojin zirga-zirgar jiragen sama na ƙasa da ƙasa.
Tsare jirgin na Najeriya ya zo ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar rashin aminta da kuma sauya ƙawance a tsakanin kashen mulkin soja a yammacin Afirka.
Kasancewar Ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar sun fice daga Ƙungiyar ECOWAS a farkon wannan shekarar ne da kuma kafa suka kafa Ƙungiyar AES ta kasashen uku.
