Sanata Muhammad Ali Ndume mai wakiltar Borno ta kudu ya ce, baya goyon bayan takarar Tinubu a 2027, saboda halin da Kasa Ke Ciki
Sanatan ya nesanta kansa daga yunkurin da wasu ke yi na nuna goyon bayan sake tsayawa takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027. Ya kuma bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin “Sunday Politics” na Channels Television a daren Lahadi.
“Halin da Najeriya take ciki a yanzu bai dace da irin wannan matsin lamba na goyon bayan siyasa ba, halin da kasa ke ciki yana da muni.”
“Matsanancin halin tattalin arziki da hauhawar farashi da kuma matsalar tsaro da ke addabar sassan kasar nan, ‘yan Najeriya ba sa ganin wani haske, kuma suna da shakku kan shirin ‘Renewed Hope’.” In ji shi.
Ndume ya kuma kawo misalin yadda tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya samu goyon bayan gwamnoni 22 daga jam’iyyarsa ta PDP a zaben 2015, amma hakan bai hana shi faduwa ba. Kuma Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya kayar da shi a wancan lokaci.
A ranar 22 ga Mayu, 2025, gwamnoni 22 na APC sun bayyana goyon bayansu ga Tinubu na ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027. Amma hakan ba shine ra’ayin talakawa ba.
