Tsohon Ministan Tsaron Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar, ya musanta rahotannin da ke yawo cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyarsa ta APC mai mulkin kasar zuwa jam’iyyar hamayya ta ADC.
A wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa, Badaru ya bayyana rahoton a matsayin labarin kanzon kurege, yana mai cewa babu wani yunkuri ko shiri a halin yanzu na barin jam’iyyar APC.
Ya kara da cewa irin wadannan rahotanni ba su da tushe balle makama, kuma an kirkiro su ne domin rudani da yaudarar jama’a, musamman mabiyansa da ’yan jam’iyyar APC.
A bangare guda kuma, a wata tattaunawa da sashen Hausa na BBC, wani hadimin tsohon Ministan Tsaro, Kwamared Abba Malami, ya ce labarin ya zo musu da mamaki matuka.
