
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi ikirarin babu wata jam’iyya ko haɗakar ‘yan adawa da za ta hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu sake komawa shugabancin ƙasar nan a zaɓen 2027.
Ganduje ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga kalaman tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar wanda ya ce, ‘yan adawa sun shirya tsaf don ƙalubalantar Tinubu a babban zaɓen 2027.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Ganduje kan wayar da kan jama’a, Cif Oliver Okpala, ya fitar, ya bayyana cewa babu wani shiri ko gungun jama’a da zai hana a sake zaɓen Tinubu.
“Ba shakka, Shugaba Tinubu zai yi nasara a 2027 saboda irin manyan ayyukan da yake gudanarwa, waɗanda ba a taɓa gani ba tun bayan hawansa mulki,” in ji Ganduje.
Ya kuma ƙara da cewa ƙoƙarin da wasu ‘yan adawa na kawar da Tinubu ba zai yi tasiri ba, yana mai jaddada goyon bayan APC ga shugabancinsa don ci gaba da aiwatar da manufofin ci gaban al’umma.
Wannan na zuwa ne yayin da siyasar 2027 ke ƙara ɗaukar zafi, inda manyan ‘yan adawa ke nuna aniyarsu ta yin gasa da Tinubu domin karɓe madafun iko.