
Babban Sufeton ‘Yansanda Kayode Egbetokun ya isa Jihar Benue domin duba halin da ake ciki bayan sabon jerin hare-haren da ake zargin makiyaya sun kai a jihar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 160 da kuma raba daruruwan mazauna da muhallansu.
Jihar Benue dai na fama da rikice-rikicen da aka shafe shekaru ana ciki, wadanda galibi ake dangantawa da rikicin kabilanci ko na fili tsakanin manoma da makiyaya.
Sai dai wannan makon ya sha bamban, inda rahotanni ke nuna cewa yawan kashe-kashen ya karu ba kakkautawa.
A ranar Lahadi, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci shugabannin hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa don dakile rikicin tare da kawo ƙarshen kisan jama’a a jihar.
A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ba za ta ci gaba da zuba ido ba yayin da rayukan mutane ke salwanta.
Fadar ta kuma tabbatar da cewa a ranar Laraba Shugaban Tinubu zai kai ziyara jihar Benue domin jajanta wa al’umma da kuma duba matakan tsaro da aka ɗauka.