
Kwalejin Koyar Da Aikin Gona ta Audu Bako a karamar hukumar Dambatta, ta musanta zargin kin bin umarnin gwamnatin Kano da kungiyar malaman kwalejin ke mata.
Kungiyar malaman kwalejojin fasaha ta kasa ASUP reshen Arewa maso yamma karkashin shugabancin Dakta Abdul’aziz Ibrahim Badaru ce ta zargi shugaban kwalejin da watsi da umarnin gwamnatin Kano na mayar da shugaban kungiyar ta ASUP reshen kwalejin bakin aiki.
Badaru ya ce, tuni gwamnatin Kano ta hannun mataimakin gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo, ta umarci kwalejin da ta mayar da shugaban bakin aiki, bayan bincike ya tabbatar da korar shi daga aiki ba bisa ka’aida ba.
A martanin shugaban Kwalejin Farfesa Muhammad Audu Wailare ya ce, sam wannan batu ba haka yake ba, domin babu wani umarni makamancin wannan da suka karba a hukumance.
Wailare ya ce shugaban kungiyar ta ASUP reshan Arewa maso yamma Dakta Abdul’aziz Ibrahim Badaru, na bata sunan kwalejin da labaran kanzan kurege game da dakatarwa da aka yiwa malamin.
Farfesa Wailare ya ce, Dr. Badaru na amfani da kafafen yada labarai wajen bata sunan shugabancin kwalejin ta hanyar yada cewa sun bujirewa umarnin gwamnatin Kano, alhali babu wani umarni makamancin wannan da ya ishe su kawo yanzu