
A wani muhimmin jawabi da ya janyo hankalin duniya, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargaɗi ga takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, cewa zai fuskanci mummunan sakamako muddin yaƙin Ukraine bai zo ƙarshe ba.
Trump ya bayyana hakan ne yayin ganawar da aka shirya gudanarwa a tsakanin su a Alaska, ranar Juma’a.
A zantawarsa da manema labarai ranar Laraba, Trump ya bayyana Putin a matsayin shugaba mara tabbas, yana mai cewa: “Yanzu zaka yi tattaunawa mai ma’ana da shi, amma da zarar ya koma gida sai ka ga ya ci gaba da kai hare-hare kan gidajen kula da tsoffi da kashe fararen hula.”
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya bayyana cewa akwai yiwuwar cimma tsagaita wuta a Ukraine, bayan da ƙawayen Ukraine a Turai suka amince da matsayar Amurka kan abubuwan da ya kamata a cimma a ganawar Trump da Putin.
Starmer ya ce wannan mataki na iya zama ginshiƙi wajen dawo da zaman lafiya a yankin.
Trump ya bayyana cewa idan ganawarsa da Putin ta kasance mai kyau, zai nemi a shirya wata ganawa ta biyu da za ta haɗa da shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky.
A cewarsa, hakan zai ba da damar tattaunawa kai tsaye da dukkan bangarorin da ke cikin rikicin.
A yayin ganawarsa da shugabannin Turai da kuma Zelensky ta kafar bidiyo, Trump ya nuna kwarin guiwa cewa ganawar da za a yi da Putin na iya zama matakin farko na share fagen warware rikicin.