Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan Kano ya rantsar da sabon shugaban hukumar yaki da rashawa da karbar korafe-korafe na jihar Kano Sa’idu Yahya.
Kwamishinan shari’a Barista Haruna Isah Dederi ne ya jagoranci rantsar da sabon shugaban da sauran masu baiwa gwamna shawara uku a fadar gwamnatin Kano ranar Laraba.
Nadin nasa ya biyo bayan karewar wa’adin shugabancin Muhyi Magaji Rimin Gado.
An kuma rantsar da Kabiru Haruna Getso da Sale Musa Sa’adu da Mr Sylvester Kole, a matsayin masu baiwa gwamna shawara a bangarori daban daban.
Da yake jawabi gwamnan Kano Abba Kabiru Yusuf ya ce an zabe su ne bisa cancanta, a don haka ya bukaci da su cigaba da jajircewa kare martabar jihar Kano.
Ya yi kira ga sabon shugaban hukumar Sa’adu Yahya ya guji nuna bangarenci tare da kaucewa cin hanci da rashawa yayin gudanar da aiki.
Gwamna Abba Kabir ya ja hankalinsa da ya guji tsoro ko barin wani yayi amfani da shi don biyan wata bukata.
Gwamnan ya godewa tsohon shugaban Muhyi Magaji bisa yadda ya gudanar da aikinsa bisa jajircewa.
Ya kuma yi kira ga sabon shugaban hukumar ya nemi shawararsa kan tafiyar da aiki.
Guraren da sabbin masu bayar da shawarar zasu yi aiki sune:
1) Kabiru Haruna Getso- SA Employment
2) Sale Musa Sa’adu- SA Social Responsibility
3) Sylvester Kole -SA South South Community
A nasa jawabi sabon shugaban hukumar yaki da rashawa da karbar korafe-korafe Sale Musa Sa’adu, ya ce zai jajirce da amfani da kwarewa wajen sauke nauyin da aka dora masa.
Shi ma Kabiru Haruna Getso da yayi jawabi amadadin sauran masu bayar da shawarar ya godewa gwamnan Kano bisa damar da ya basu.
Ya ce zasu yi aiki bisa kwarewa don sauke a guraren da aka sanya su daban daban.


