Hukumar zabe ta kasa INEC ta bude zagaye na uku na rajistar masu zabe anan Kano, na bude rajistar ne a Litinin din nan 11 ga watan Mayun 2026.
Sanarwar da hukumar ta fitar tayi kira ga wadanda basu yi rajistar ba, ko wadanda tasu ta bata, ko wadanda suka kai shekara 18 yanzu, su garzaya cibiyoyin rajistar domin ayi musu.
Ana sa ran wannan shi ne karo na karshe da INEC zata yi rajistar masu zabe kafin zaben 2027, za a kammala aikin sabunta rajistar ranar 10 ga watan Yulin 2026.
