Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya karɓi katin zama dan jam’iyyar ADC wanda hakan ya tabbatar da koma wa jam’iyyar a hukumance.
Atikun ya yi rajistar zama tabbataccen ɗan jam’iyyar ADC ne a mazaɓarsa ta Jada da ke jihar Adamawa.
Ya kuma da sanar da hakan ne a shafinsa na X, inda ya wallafa hotuna riƙe da katin sabuwar jam’iyyarsa, da gajeren rubutu da ke nuna ya shiga jam’iyyar a hukumance.
A ranar 14 ga watan Yulin 2025 ne cikin wata sanarwa Atikun ya bayyana ficewa daga PDP ba tare da ɓata lokaci ba.
Tun a wancan lokacin dai Atikun ya kuma ce wajibi ne ya raba gari da jam’iyyar ta PDP bisa la’akari da yadda ta sauka daga tubalinta na asali.
Atiku ya yi wa jam’iyyar PDP takarar kujerar shugaban ƙasar Zaɓen 2023, ya kuma zama mataimakin shugaban kasa na shekara takwas da aka zabe su tare da Obasanjo.
