Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU na shirin sake komawa yajin aiki bayan da ta zargi gwamnati da rashin cika alkawarinta, na biya musu bukatunsu da suka daɗe suna nema.
Wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Christopher Piwuna ya fitar, ƙungiyar ta nuna damuwa kan rashin kula da walwalar mambobinta, rashin kuɗaɗen gudanarwa da kuma rashin cika alkawura da aka amince da su.
Gargaɗin dai na zuwa ne bayan da ministan ilimin ƙasar Dakta Tunji Alausa, ya ce babu wata jami’a ko malaman ASUU da za su sake shiga yajin aiki a Najeriya, duba da yadda gwamnati ta dukufa wajen cika alkawuran malaman da kuma shiga tattaunawa dasu.
Sai dai ASUU ta ce idan ana son kauce wa yajin aiki to a cika musu alkawuran da aka amince da su.
Ƙungiyar ta ce yawancin malamai na koyarwa ne ba tare da wani abu ya shiga cikinsu ba, kuma suna gudanar da bincike-bincike ba tare da samun abubuwan da suka kamata ba.
