Jam’iyyar APC ta buƙaci Ministan Abuja, Nyesom Wike, da ya ajiye muƙaminsa ya mayar da hankali kan siyasar Jihar Rivers, idan hakan ne ya fi masa muhimmanci.
Sakataren Jam’iyyar APC na Ƙasa, Ajibola Basiru, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce jam’iyyar ta fahimci cewa Wike na nuna sha’awa wajen tsoma baki a harkokin da ba su shafe shi ba, maimakon ya mayar da hankali kan nauyin da aka ɗora masa a matsayin minista.
Basiru ya jaddada cewa Wike ba shi da wani hurumi ko iko na tsoma baki a harkokin APC, kasancewar ba mamba ba ne a jam’iyyar.
Martanin na APC ya biyo bayan kalaman gargaɗi da Wike ya yi a yayin wata ziyarar “godiya” da ya kai Ƙaramar Hukumar Oyigbo a Jihar Rivers, inda ya gargadi Sakataren APC na Ƙasa da ya nisanci siyasar jihar.
Wike ya kuma zargi wasu da zuwa Rivers ne domin neman cin gajiyar kuɗaɗen jihar.
A cewar Basiru, matsayinsa na Sakataren APC na Ƙasa ya ba shi cikakken ikon kula da harkokin jam’iyyar a duk faɗin Najeriya, ba a Jihar Osun kaɗai ba, kamar yadda Wike ya yi nuni da hakan.
