Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa da Gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Kano ya yi watsi da zargin tsoma baki a hukuncin Kotun Ƙoli da ya tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf a zaɓen shekarar 2023.
A wata sanarwa da kakakin kwamitin, Hon. Sanusi Kiru, ya sanya wa hannu, APC ta bayyana ƙorafin a matsayin wanda bai ƙunshi gamsassun hujjoji ba.
Ƙorafin, wanda aka ce Comrade K. Suleiman ya gabatar a madadin ƙungiyar Concerned Nigerian Citizens, ya buƙaci Majalisar Kula da Harkokin Shari’a ta Ƙasa NJC ta gudanar da bincike kan zargin.
Batun ya samo asali ne daga wata hira da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi da BBC Hausa, inda ya bayyana cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya umurce shi da ya tuntuɓi Shugaba Bola Tinubu dangane da shari’ar zaɓen gwamnan Kano.
Sai dai kwamitin APC ya ce abin da gwamnan ya bayyana shi ne neman shugaban ƙasa kada ya tsoma baki a shari’ar, ba wai neman ya sauya hukuncin kotun ba.
Kwamitin ya kuma ƙalubalanci masu ƙorafin da su gabatar da hujjojin da ke tabbatar da cewa an tuntuɓi wani alƙalin Kotun Ƙoli ko kuma an aikata wani abu da ya saɓa wa ƙa’ida domin sauya hukuncin.
APC ta buƙaci NJC ta tantance ƙorafin idan an gabatar da shi a hukumance, tare da yin watsi da shi idan bai cika ƙa’idojin shari’a da na gabatar da hujjoji ba.
