Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya gana da tawagar haɗin gwiwa daga Hukumar zuba jari ta ma’aikatar kuɗin Najeriya da kamfanin Mota-Engil, gabanin bikin sanya harsashin aikin titin jirgin ƙasa a cikin ƙwaryar birnin Kano, wanda Shugaba Bola Tinubu ya amince da aiwatarwa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar,
inda sanarwar ta ce tawagar ta gana da gwamnan ne a gidan gwamnatin Kano da ke Abuja domin yi masa bayani kan shirye-shiryen fara aikin.
Sanarwar ta ce an amince da aikin ne kan kuɗi naira tiriliyan ɗaya da biliyan hamsin, kuma ana sa ran zai inganta harkokin sufuri a cikin birnin Kano, rage cunkoson ababen hawa, da kuma bunƙasa harkokin tattalin arziƙi a faɗin jihar.
Da yake yiwa tawagar jawabi, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da haɗa kai da Gwamnatin tarayya da kamfanin da zai aiwatar da aikin domin tabbatar da kammala shi cikin nasara.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na godewa Shugaba Tinubu, bisa amincewa da aiwatar da aikin a Kano, tare da yabawa Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Bichi, kan irin gudunmawar da ya bayar wajen samun goyon bayan majalisa domin ganin aikin ya tabbata.
