Rahoton bashin ya fito ne daga ofishin Kula Da Basuka na Kasa.
Rahoton da ofishin ya fitar ya nuna cewa jihohin Arewa maso Yamma sun tara bashin cikin gida da ya kai Naira biliyan 254.
Jihar Zamfara ce ke kan gaba da Naira biliyan 60.6, sai Sokoto da Naira biliyan 58.8.
Jihar Kano ita ce mafi yawan bashi baki ɗaya, tana da Naira biliyan 61.9.
Sauran jihohin sun haɗa da Kaduna (Naira biliyan 26.6), Katsina (Naira biliyan 30.5), Kebbi (Naira biliyan 15.3), yayin da Jigawa ke da mafi ƙarancin bashi da Naira biliyan 1.2.
A bangaren bashin waje kuwa, Jihar Kaduna ce ke kan gaba har zuwa watan Yuni 2024.
Rahoton ya haifar da damuwa kan yadda jihohin ke ci gaba da dogaro da bashi, lamarin da ke barazana ga ci gaban tattalin arzikinsu.