Wasu matasa sun yi daga jihar Zamfara da sun gudanar da zanga-zangar kan matsalar tsaro da kuma bukatar sauke minista Bello Matawalle.
Matasa da suka hada da maza da mata sun gudanar yi zanga-zangar ne a shalkwatar tsaro ta kasa dake babbar birnin tarayya.
Matasa sun ce sun fito ne la’akari da karuwar ayyukan ta’addanci a jihar, da ma yankin arewa maso yammacin kasar nan.
Mai magana da yawun masu zanga-zangar, Malam Musa Mahmoud, ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya gaggauta sauke karamin ministan tsaro, tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, domin a cewarsa, nadinsa babu abin da ya haifar sai karuwar ayyukan ta’addanci a jiharsu.
Shugaban wanda kuma shi ne shugaban APC ‘akida’ a jihar Zamfara, ya ce suna fatan idan an sauke ministan a kuma bincike shi.
Zanga-zangar na zuwa ne bayan da jam’iyyar APC a jihar ta bukaci shugaban kasa ya kasa ya ayyana dokar ta-baci a bangaren tsaro.
Hakan a cewar su, zai ba jami’an tsaro damar kawo karshen bata-garin dake ci gaba da addabar jihar.