
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shiyyar arewa maso yamma ce ke da kaso mafi tsoka na kuɗaɗen da aka ware wa manyan ayyukan ci gaba a Najeriya.
Ministan Yaɗa Labarai, Muhammad Idris ne ya bayyana hakan a ranar Litinin.
A matsayin martani ga rahoton wata jarida da ta nuna cewa jihar Lagos, wacce ke kudu maso yamma, ta samu kuɗaɗe fiye da jihohi 18 da ke yankunan kudu maso gabas da arewa maso yamma da kuma arewa maso gabas cikin shekaru biyu da suka gabata.
“An amince wa shiyyar arewa maso yammacin kusan naira tiriliyan 6, wanda ya kai kashi 40 cikin ɗari na jimillar kuɗaɗen da aka ware domin gudanar da ayyuka a matakin tarayya”. In ji shi
Ministan ya kuma bayyana cewa, bayan arewa maso yamma da ta samu kashi 40 cikin ɗari na kuɗaɗen ayyuka, yankin arewa ta tsakiya ya samu kusan Naira Tiriliyan 1 da Biliyan 1, yayin da jihar Lagos ta samu kusan Naira Tiriliyan 1 da Biliyan 2.
Idris ya kuma bayyana cewa babban dalilin da yasa jihar Lagos ta samu kuɗaɗe da yawa shi ne saboda kasancewar ta da manyan gadoji da tasoshin jiragen ruwa da kuma filin jirgin sama mai fadi, waɗanda ke buƙatar kulawa da gina manyan ayyuka na ci gaba.