Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta sanar da dokar takaita zirga-zirgar dare a fadin jihar domin dakile ayyukan laifi.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Ya ce, dokar za ta fara aiki ne daga ranar Jumu’a, 7 ga Fabrairu, daga karfe 12 na dare zuwa 5 na Asuba a kowacce rana.
Sanarwar ta ce, matakin ya biyo bayan bayanan sirri da ke nuna yunkurin aikata miyagun laifuka, musamman a cikin dare.
Rundunar ta gargadi iyaye da su ja kunnen yaransu don gujewa karya dokar, wanda ka iya kai su ga fuskantar hukunci.
