
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa an samu sauƙin hauhawar farashi a Najeriya, inda rahoton ta na watan Yuni 2025 ya nuna cewa hauhawar farashin ya ragu zuwa kaso 22.22% idan aka kwatanta da kaso 22.97% a watan Mayu.
A cewar rahoton, idan aka kwatanta da irin wannan lokaci a shekarar 2024, an samu raguwar hauhawar farashi da kaso 11.97%. Wannan na nuna ɗan sassauci a matsin da jama’a ke fuskanta, musamman a ɓangaren abinci da sauran kayan masarufi.
Bayan cire tallafin man fetur a shekarar da ta gabata, farashin kayayyaki ya yi tashin gwauron zabo, lamarin da ya jefa miliyoyin ’yan ƙasa cikin ƙuncin rayuwa.
Sai dai masana sun bayyana cewa, wannan sabuwar raguwar hauhawar na iya zama alamar farfadowar tattalin arziki idan aka ci gaba da tafiya a wannan turba.