Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta bayyana damuwa kan ƙaruwar sace-sacen mutane a sassan Najeriya, inda ta ce an sace mutane aƙalla 1,100 a tsakanin watan Janairu zuwa Afrilun 2026, kuma mafi yawa a jihohin Arewa.
Amnesty International ta ce dole ne gwamnain shugaba Bola Tinubu ta gaggauta ɗaukar matakan magance wannan matsala da ke ƙara muni, musamman a tsakanin al’ummar karkara da mazauna sansanonin ƴan gudun hijira.
Sunusi ya ce mutane mafi yawa da aka sace a lokaci guda su ne a jihar Borno, a wani gari da ake cewa Ngoshe da ke karamar hukumar Gwoza, inda ƴan Boko Haram suka sace mutane fiye da 300. Sannan kuma akwai mutane kusan 200 da aka sace a Woro a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara.
Ya kara da cewa akwai wadansu kuma a jihar Zamfara aka sace mutum 150 a ƙaramar hukumar Bukkuyum, inda aka ce mafi yawan waɗanda abin ya shafa mata ne da yara.
Daraktan ƙungiyar Amnesty a Najeriya ya ce wannan alƙalumman da aka tantance ne kuma aka tabbatar da su, amma ”akwai inda ake sace mutanen da ba a jin labari saboda suna faruwa ne a wurare masu nisa, da suke nesa da kafofin yaɗa labara.
