Mahukunta a Ghana sun rufe sama da gidajen rediyo 60 da aka zarga da karya ƙaidoji.
Gidajen Rediyon da suke alaƙa da fitattaun ƴan adawa abin ya shafa.
Hukumar da ke kula da kafafaen yada labarai ta ce wasu daga cikin ba su da izinin ko kuma ba su sabunta lasisinsu ba.
Shugaban Ƙungiyar Ƴan Jaridu ta Ghana Albert Kwabena Dwunfour ya ce akwai buƙatar a cire siyasa a batun bayar da izinin kafafen yaɗa labarai.
Akwai fiye da gidajen Rediyo ‘dari biyar a Ghana.
