An rufe rumfunan zaɓe a zaɓen shugaban ƙasar Ivory Coast, wanda shugabar kasar mai ci Alassane Ouattara ke neman wa’adi na huɗu na shekara biyar.
An kaɗa ƙuri’a cikin kwanciyar hankali a wurare daban daban, sai an samu dan tashin hankali a wasu wuraran wanda aka lalata akwatinan zaban.
Ana sa ran samun sakamakon zaɓen nan da ranar Alhamis mai zuwa, inda dole sai ɗan takara ya lashe fiye da kashi 50 cikin 100 na ƙuri’un kafin ya yi nasara.
Wasu daga ciki masu katin zaɓe sun bi umarnin ‘yan’adawa wajan ƙin fita kaɗa ƙuri’a, wanda ake ganin ya taimaka wajen ƙarancin yawan masu kaɗa ƙuri’ar.
