Tsohon Shugaban Hukumar Kaɓar Koke-koke da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya ce an kama shi ne saboda jagorantar shari’ar almundahanar biliyoyin Naira na Dala Inland Dry Port, da ta shafi Ganduje da iyalinsa.
A hirarsa da DCL Hausa bayan an sako shi, ya ce, ’yan sandan sun ƙi nuna masa takardar izinin kama shi har sai da suka isa Abuja.
To tuni dai an bayar da belinsa, amma an umarce shi da ya koma Abuja a ranar Laraba tare da miƙa fasfo dinsa.
Ganduje da ’ya’yansa na fuskantar shari’a kan zargin canja mallakar kaso 20 na hannun jarin jihar Kano Tashar Tsandauri Dala Inland Dry Port.
