
Jami’an tsaron ƙasar Saudiyya sun cafke wasu mata biyu da ake zargin su ne matar da kuma mahaifiyar fitaccen shugaban ’yan bindiga da gwamnatin Najeriya ke nema ruwa a jallo, Ado Aliero.
An kama su ne a birnin Madina yayin da suka je ziyara kafin fara aikin Hajji.
Rahotanni daga majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa matan sun sauya sunayensu domin kauce wa hukumomi, amma hakan bai hana jami’an tsaro gano ainihin su ba.
Wannan na ɗaya daga cikin jerin matakan da hukumomin tsaro na ƙasashen duniya ke ɗauka tare da haɗin gwiwar Najeriya domin dakile ayyukan ta’addanci da na ’yan bindiga a kasar.
Ado Aliero, wanda aka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin fitattun shugabannin kungiyar masu garkuwa da mutane a yankin arewa maso yammacin Najeriya, musamman a jihar Zamfara, ya shahara wajen gudanar da hare-hare da sace-sacen mutane.
