
Bayanai daga rundunar sojin kasar nan na cewa an kafa wani kwamiti da ke binciken wasu jami’ai 20 da aka tsare bisa zargin yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Jaridar Premium Times ta ruwaito wata majiyar soji da ke da masaniya kan lamarin tana cewa al’amarin ya faru ne a ƙarshen watan Satumba.
Majiyar ta ce ana zargin jami’an da shirya zubar da jini a juyin mulkin, kasancewar akwai sunayen wasu manyan jami’an gwamnati da aka shirya yi wa kisan gilla.
Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, daga cikin manyan jami’an gwamnatin waɗanda masu kitsa juyin mulkin suka shirya yi wa kisan gilla akwai shugaba Bola Tinubu da matamaikinsa, Kashim Shettima da kuma shugabannin Majalisun Tarayya, Sanata Godswill Akpabio da Abbas Tajudeen da sauransu.
Waɗanda ake zargin dai, bayanai sun tabbatar da cewa sun tsayar da ranar da za su kifar da gwamnatin farar hula, yayin da suke tuntuɓar juna a kai a kai.
Wannan yunƙuri na juyin mulkin ya haifar da firgici a tsakanin manyan jami’an gwamnati bayan da aka fallasa shi, duk da cewa babban hafsan sojin ƙasar ya sha ba wa gwamnatin Najeriyar tabbacin goyon bayan sojoji ga gwamnati.