Dubban masu zanga-zanga ne suka hallara a belgrade, babban birnin serbia jiya asabar inda suke neman a matso da lokacin zaɓe gaba tare da kawo ƙarshen gwamnatin shugaba aleksandar vucic.
A ɗaya daga cikin manyan gangamin da aka yi na tsawon watanni ana zanga-zangar ƙarƙashin jagorancin ɗalibai, dandazon al’umma sun cika wani dandali da tituna maƙil.
Wasu sun yi arangama da ƴansandar kwantar da tarzoma a lokacin da suke tsaka da gudanar da zanga-zangar, wadda suka ce ta lumana ce.
Shi dai shugaba vucic ya zarge su da ƙoƙarin kifar da gwamnati.
Magoya bayan shugaban ƙasar suma sun taru domin gudanar da tasu zanga-zangar a kusa da majalisar dokokin ƙasar.
Ɗaliban dai sun zargi shugaban ƙasar serbia da makusantansa da tafka rashawa da kuma tauye ƴancin kafafen yaɗa labarai.
