Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) reshen jihar Kano, tare da haɗin gwiwar gidauniyar EL’s Foundation, sun gudanar da tattakin wayar da kai domin fadakar da matasa kan illolin amfani da kwayoyi.
Tattakin ya gudana a cikin manyan titunan Kano, inda mahalarta suka ɗauki alluna masu ɗauke da saƙonni na gargadi da faɗakarwa.
Tattakin, wanda ya fara daga hedkwatar NDLEA da ke titin Airport Road, ya samu jagorancin mataimakin kwamandan hukumar, Aliyu Isa Dabo (DCN), wanda ya wakilci kwamanda CN Ahmad.
A cewarsa, wannan tattaki wata hanya ce ta haɗa kai da hukumomin gwamnati, kungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki wajen yaki da matsalar shaye-shaye a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
Wakiliyarmu Safina Abdullahi Hassan ta rawaito cewa hukumar NDLEA ta nuna godiya ga EL’s Foundation bisa haɗin gwiwar da suka bayar, tare da jaddada aniyarta na ci gaba da ƙirƙirar dabarun rigakafi da za su taimaka wajen gina al’umma mai koshin lafiya da wayewa.
