Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC) ta dakatar da aikin sabunta rajistar masu zaɓe, bayan korafe-korafe daga ’yan siyasa da masana.
Hukumar ta umarci kwamishinoninta na jihohi su dakatar da duk wani shiri na aikin, har sai abin da hali ya yi
Tun da farko Jam’iyyar ADC da PDP sun nuna damuwa cewa aikin zai iya hana miliyoyin ’yan Najeriya kaɗa ƙuri’a kafin zaɓen, musamman a Arewa.
Sai dai wasu da wakiliyarmu Khadija Iliyasu Kore ta tattauna dasu sun nuna rashin jin dadinsu da soke aikin rajistar, dai dai lokacin da suka ce suna kokarin fita domin sabunta ta su.
Wasu masana sun yi gargaɗi kan cewa ƙurewar lokaci da rashin isassun kayan aiki na iya rage halartar masu zaɓe.
Amma INEC ta bayyana cewa aikin na da nufin tabbatar da ingantacciyar rajista, ba don hana kowa kaɗa kuri’a ba.
