
Daga Khalil Ibrahim Yaro
Da farko an shirya sarkin zai kai ziyara wasu kananan hukumomin jihar 5
Majalisar Masarautar Kano ta sanar da dage rangadi da Sarkin Muhammad Sunusi II zai fara zuwa wasu kananan hukumomin jihar a yau Jumma’a
Shugaban Ma’akatan Fadar Sarkin Alhaji Aliyu Ibrahim Ahmad kuma Matawallen Kano ne ya bayyana dagewar a wata takarda mai dauke da sa hannunsa aka kuma yada a kafafen yada labarai.
Matawallen ya ce, dage rangadin ya biyo bayan wata tattaunawa ne fadar ta yi da gwamnatin Kano da kuma rashin kammala wasu shirye-shirye na rangadin.
An shirya sarkin zai kai rangadin zuwa wasu kananan hukumomi biyar a inda zai soma da Danbatta da kuma Makoda a ranar Juma’a ya kuma kare da Ungoggo a ranar Litinin.
Ana kuma sa rai a yayin ziyarar zai halarci saukar karatu daliban makarantun Islamiyya da kuma wasu ayyuka na kasa.
Sanarwar ta kuma ce a jira ta nan da dan wani lokaci kadan don sanar da sabbin ranakun rangadin da kuma Kananan Hukumomin da za a je.