Al’ummar garin Kanye dake Karamar Hukumar Kabo sun nuna damuwarsu kan yadda jami’an Ma’aikatar Kasa Da Tsare-Tsare Ta Jihar Kano ke auna gonaknsu da gidajensu sama da 2000, ba tare da biyansu diyya ba.
Al’ummar garin sun bayyan haka ne ga wakilinmu a yayin da ya kai ziyara garin a ranar Talata.
“Bukatar gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da ya shiga cikin lamarin domin ganin an biyamu hakkokinmu wanda hakan zai taimaka mana wajen daukar nauyin kula da iyalansu tare da mallakar wani muhallin”. In ji wani magidanci.
A tattaunawar wakilinmu da Daraktan Wayar Da Kan Al’umma na ma’aikatar, Murtala Shehu Umar, ya ce mutanen garin sun gajen hakuri.
“Tuni gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sahale da a biya al’ummar garin wadanda abin ya shafa diyyar kadarorin nasu”. In ji shi.
Daraktan ya kuma yi kira da su kwantar da hankalinsu, gwamnatin Kano za ta biya su diyyar nan ba da jimawa ba.
