Fadar White House ta sanar da cewa Amurka za ta dakatar da bayar da bizar ƴan ci rani ga ƴan ƙasashe 75, a wani mataki da ta ce yana da nasaba da sake duba tsarin tantance masu neman shiga ƙasar.
Ƙasashen da dakatarwar ta shafa sun haɗa da Rasha, Iran, Afghanistan, da wasu ƙasashen Afirka, haka kuma Thailand da Brazil.
A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar, an umurci dukkan ofisoshin jakadancinta da su dakatar da bayar da irin waɗannan biza, yayin da ake ci gaba da yin cikakken bita kan matakan da ake bi wajen tantacewa.
Sanarwar ta bayyana cewa dakatarwar za ta fara aiki ne cikin mako guda, amma ba a fayyace tsawon lokacin da za a ɗauka kafin a janye ta.
