Rahotanni sun bayyana cewa Amurka ta kama tsohon Ministan Kuɗi na Ghana, Ken Ofori-Atta.
Wata sanarwa da tawagar lauyoyin sa ta fitar ranar Laraba ta bayyana cewa lauyoyin na tuntuɓar hukumar ICE, kuma suna sa ran za a warware matsalar cikin gaggawa.
Ofori-Atta da wasu mutum bakwai suna fuskantar tuhuma guda 78 kan kwangilolin da aka bai wa kamfanin Strategic Mobilisation Ghana Limited (SML).
A bisa tuhumar da Ofishin Mai Gabatar da Ƙara na Musamman (OSP) ya shigar a watan Nuwamba 2025, ana zargin mutanen da almundahanar kuɗaɗen sayo kayayyakin da aka bai wa SML kwangila don kaiwa Ghana.
Bugu da ƙari, an zarge su da ƙoƙarin amfani da Ma’aikatar Kuɗi ta Ghana da Hukumar Tattara Haraji ta Ghana.
Ken Ofori-Atta ya kasance a Amurka tun daga watan Janairu 2025 saboda neman lafiya.
Duk da haka, ofishin mai gabatar da kara wato OSP ya sanya shi karkashin ‘yansandan ƙasa da ƙasa a matsayin mutumin da ake nema ruwa-a-jallo saboda amfani da ofishin gwamnati don amfanin kansa, matakin da Ofori-Atta ya musanta.
