Amurka ta ce Isra’ila da Siriya sun amince da tsagaita wuta wadda ƙasashen Amurkan da Turkiyya da Jordan suka shiga tsakani.
Sanarwar na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan Isra’ila ta kaddamar da hare-hare ta sama a Damascus babban birnin Siriya.
Sai dai Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a kudancin lardin Sweida na kasar Siriyan da ke cikin wani mummunan tashin hankali mai nasaba na kabilanci tsakanin al’ummomin Druze da Bedouin.
mutane a Swieda sun bayyana yadda gawawwaki ke jibge a kan tituna da kuma yadda aka yi wa wasu mutane kisan gilla.
Sama da mutum 600 ne aka kashe a Sweida tun ranar Lahadi kuma hukumomin kasar Syria sun ce za su tura dakaru na musamman domin kawo karshen fadan.
