Majalisar wakilan Amurka ta bukaci ma’aikatun harkokin wajen ƙasar da na kuɗi su kakaba takunkumi na musamman ga wasu mutane da kungiyoyi a Najeriya da ake zargin suna da hannu wajen take hakkin ’yancin addini, ciki har da Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria da Miyetti Allah Kautal Hore.
Wannan bukatar na cikin wani ƙuduri da ɗan majalisa Christopher Smith ya gabatar, wanda ya yaba wa shugaban Amurka Donald Trump bisa matakinsa na sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake ganin suna da “matsala ta musamman” wajen ’yancin addini, musamman kan zargin tsananta wa Kiristoci da ƙananan ƙungiyoyin addini.
A cewar ’yan majalisar, ƙudurin ya samo asali ne daga rahotanni na ƙungiyoyi masu zaman kansu da kafofin yada labarai, waɗanda ke zargin wasu kungiyoyin Fulani da kai hare-hare, kashe-kashe da sace-sace a jihohi da dama, musamman Benue da Plateau, tare da lalata coci-coci da wuraren ibada.
Ƙudurin ya kuma ba da shawarar cewa Amurka ta janye tallafinta ga gwamnatin Najeriya, tare da karkatar da agajin jin ƙai kai tsaye zuwa ga mutanen da abin ya shafa.
Sai dai a martaninsa, ministan yada labarai na Najeriya, Mohammed Idris, ya soki wannan mataki, yana mai cewa barazanar da ake yi ta samo asali ne daga “ɓatanci da rashin sahihan bayanai.”
Ya jaddada cewa matsalar ta’addanci da rashin tsaro a Najeriya ba ta shafi addini guda ɗaya ba, domin tana shafar Kiristoci da Musulmai baki ɗaya.
Ministan ya ce gwamnatin Najeriya ba ta goyon bayan kowanne irin cin zarafi ko wariyar addini, kuma tana ci gaba da ɗaukar matakai don tabbatar da zaman lafiya da adalci ga kowa.
