Wakilan Amurka da Rasha sun yi wata tattaunawa a birnin Abu Dhabi na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, a wani sabon yunƙuri da gwamnatin Donald Trump ke yi na kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.
Sakataren Rundunar tsaron Amurka Dan Driscoll ne ya jagoranci tattaunawar, wadda mista Trump ke fatan za a kai ga kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru ana gwabzawa tsakanin kasashen da ke makotaka da juna.
Wakilan Amurka da Ukraine na kokarin cimma manufofin da suka tunkara kan shirin zaman lafiya, inda har yanzu ba a warware wasu manyan batutuwa ba, kuma Ukraine na fargabar amincewa da yarjejeniyar bisa sharuddan Kremlin.
Ba a fayyace ainihin yanayin tattaunawar ba, sannan babu masaniya kan wanene ke jagorantar tawagar Rasha ba.
Abin da bayanai ke nuna wa shine, manufar Amurka a kawo karshen yakin a cikin wannan wata.
Manufofin da Amurka ta zo da su, sun haifar da fargabar cewa gwamnatin Trump za ta iya sanya Ukraine ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar da za ta amfani Rasha kadai.
Shirin zai bukaci Kyiv ta mika karin yankuna, ta amince da takaita sojojinta, sannan ta ajiye mafarkinta na shiga NATO, sharuɗɗan da gwamnatin Kyiv ta dade tana kin amincewa da su.
