
Ta na yin hakan ne ta karkashin Hukumar Raya Kasashen (USAID) inji dan Majalisar Wakilan kasar
Mista Perry, dan jam’iyyar Republican mai wakiltar Pennsylvania ya yi wannan ikirarin ne a ranar Alhamis.
A kuma yayin taron sauraron ra’ayin na wani karamin kwamiti kan ingancin ayyukan gwamnati wanda ya mayar da hankali kan zargin karkatar da kudaden masu biyan haraji, da gwamnati ke yi da sunan agaji, zuwa ga wasu ayyyuka nan daban.
“Dala miliyan 697 a duk shekara USAID ta ke kashewa, da kuma safarar kudade kungiyoyin ISIS da Al-Qaeda da Boko Haram da Khorasan, da kuma sansanonin horar da ’yan ta’adda.” In ji shi
Terrry ya kuma ce, hukumar ta USAID ta bayar da Dala miliyan 136 don gina makarantu 120 a Pakistan, inda ya yi zargin babu wata shaida ko da ke nuna gina makarantun.
A Najeriaya, kungiyar Boko Haram ta kwashe sama da shekaru 15 tana kai hare-hare a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya inda ta kashe dubun-dubatar jama’a ciki har da ‘yan sanda da sojoji da kuma fararen hula.
Hare-haren kungiyar sun yi sanadin mutuwar yara fiye da 300,000 da raba mutune miliyan 2.3 da gidajensu da kuma haifar da matsalar abinci da yunwa a yankin.
Shafin Aminiya ya rawaito cewa, Shugaba Donald Trump ya bayar da umarnin rufe hukumar ta USAID, kan zargin ta da cin hanci da rashawa a wani sako da ya wallafa.
Shi ma Elon Musk, abokin Trump, kuma shugaban ma’aikatar kula da ayyukan gwamnati, ya soki hukumar ta USAID, yana mai zargin cewa tana gudanar da ayyukan damfara.
Daga cikin wasu sukar, Musk ya yi iƙirarin cewa USAID tana “aikin leken asiri kamar CIA” har ma da “binciken kuɗaɗen binciken makaman ƙare-dangi, gami da COVID-19, wanda ya kashe miliyoyin mutane.”