Kasar Amruka ta sanar da ficewa daga Hukumar kula da Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya, UNESCO.
Ba wannan ne karon farko da Washington ke fita daga UNESCO ba, domin ko a shekarar 2018 sai da shugaba Donald Trump ya fitar da ƙasar daga cikinta, kafin dawowarta a shekarar 2023, ƙarƙashin mulkin Joe Biden.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gidan Amurka, Tammy Bruce ta ce zaman ƙasar cikin UNESCO baya cikin muradunta, tana mai cewa hukumar na nuna ƙiyayya ga Isra’ila, tare da haifar da rarrabuwar kawuna.
Tammy ta ce matakin UNESCO na amincewa da samar da ƙasar Falasɗinu na cike da kura-kurai, kuma yaci karo da muradun Amurka, abinda ya haifar da furta kalaman rashin goyon bayan Isra’ila a cikin ƙungiyar.
Matakin ficewar da Amurka ta ɗauka zai fara aiki ne a ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2026.
UNESCO ta nuna rashin jin daɗinta da matakin da Trump ya ɗauka na ficewa daga cikinta, a cewar babbar daraktar hukumar Audrey Azoulay.
