
Kansa a kasa tayoyinsa a sama, bai kama da wuta ba, bai kuma tarwatse ba kamar yadda aka saba gani a hatsarin jiragen sama irin wannan.
Wasu fasijonjin jirgin sama sun tsallake rijiya da baya yayin da jirgin da suke ciki ya tuntsire, wani sashinsa kuma ya kama da wuta a yayin sauka.
Lamarin ya faru ne a kasar Canada a ranar Talata a filin jirgin saman Toronto Pearson.
Jirgin saman na Kamfanin Delta Air mai dauke da fasinjojin 80 ya taso ne daga Minneapolis a Amurka, ya kuma yi kokarin sauka ne a filin jirgin saman Toronto.
Ana kyautata zaton santsi ne daga dusar kankarar da aka share ya kwashi jirgin ya kuma tunsira kansa a kasa, tayoyinsa a sama.
John Nelson wani fasinjan cikin Jirgin da lamarin ya rutsa da shi, ya bayyana yadda suka ji a hirarsa da ‘yan jaridu da kuma shafinsa na Facebook bayan faruwar lamarin.
“Mun sauka a filin jirgin lafiya, amma a lokacin da ya ke gudu zuwa inda zai tsaya sai muka ji ya kada gefe guda da iska mai karfi ta debi shi, sai muka ji wata mummunar kara, kuma wuri ya hargitse yayin da kawunanmu suka koma kasa.
“Wuta ta tashi, ma’aikatan ceto suka bude wata kofa mu ka yi ta kokarin fitowa. Wani sashe na jirgin ya kone amma ina jin dukkaninmu mun fita. Inji shi.
Jirgin na faduwa jami’an kashe gobara da sauran masu bayar da agaji suka yi cincinrindo a wurin domin ceto da kuma bayar da ayyukan agajin gaggawa.
Ma’aikatan bayar da agajin gaggawa sun ce, mutane Takwas ne suke samu kananan raunuka, kuma babu wanda ya bace daga adadin fasinjoji da ma’aikatan jirgin.
Hukumar Kula da Filin Jirgin Saman ta ce, za ta gudanar da bincken musabbabin hadarin kuma za ta sanar da jama’a.