
Hadimin Na Musamman Ga Shugaba Tinubu Kan Harkokin Sadarwa, Abdulaziz Abdulaziz ya bayyana cewa, akwai alaƙa dadaddiya ta siyasa tsakanin Tinubu da Rabiu Musa Kwankwaso, don haka babu wani laifi idan suka sake haɗa kai a yau.
Abdulaziz ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da ya yi da manema labarai, inda ya ce tun kafin yau, Tinubu da Kwankwaso sun sha yin aiki tare a manyan matakan siyasa, daga zama sanatoci a 1993, zuwa zama gwamnoni a shekarar 1999.
“Shugaba Tinubu da Injiniya Kwankwaso sun daɗe da sanin juna. Sun zauna a Majalisar Tarayya a shekarar 1993 a matsayin zaɓaɓɓun ‘yan majalisa. Haka kuma an zaɓe su a matsayin gwamnoni a lokaci guda a 1999. Wannan ya tabbatar da cewa akwai dangantaka ta siyasa mai ƙarfi a tsakaninsu.” In ji shi.
Abdulaziz ya kuma ƙara da cewa, yin haɗin gwiwa tsakanin ‘yan siyasa al’ada ce da ke cikin tsarin dimokuraɗiyya kuma babu wani laifi ko abun ɓoye wa idan shugaban ƙasa ko wasu daga cikin abokansa suka zauna da Kwankwaso don tattaunawa.
“Hadaka tsakanin ‘yan siyasa ba laifi ba ne. Ko fadar shugaban ƙasa ta gana da Kwankwaso, ba laifi aka aikata ba. A siyasa, tattaunawa da haɗin gwiwa abu ne na yau da kullum,” in ji hadimin