Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi watsi da zargin cewa an yi canji ga sababbin dokokin haraji bayan Majalisar Tarayya ta amince da su.
Akpabio ya bayyana cewa dokokin da aka wallafa a jaridar gwamnati, kuma Shugaban Ƙasa ya sanya wa hannu, sun yi daidai da ƙudurorin da ’yan majalisa suka amince da su a duka ɓangarorin majalisar.
Ya yi wannan bayani ne a yayin zaman Majalisar Dattawa, a matsayin martani ga ikirarin da ɗan Majalisar Wakilai, Abdussamad Dakuku, ya yi.
Shugaban majalisar dattawan ya ce zargin ba shi da tushe, yana mai jaddada cewa duk wata takarda da ba Majalisar Tarayya ce ta fitar da ita ba tare da tantancewa ba, ba za a ɗauke ta a matsayin sahihiya ba.
Ya ƙara da cewa dokokin sun fito ne bayan dogon nazari a majalisar dattawa da majalisar wakilai, sannan an sasanta dukkan bambance-bambancen da ke tsakanin bangarorin biyu kafin a kammala aikin.
Akpabio ya ce dokoki huɗu da suka shafi haraji sun bi dukkan matakan da doka ta tanada, majalisar ta amince da su, Shugaban Ƙasa ya sanya hannu, sannan aka wallafa su a hukumance.
Ya yi gargaɗin cewa kada a fitar da dokokin ta hanyoyin da ba na hukuma ba, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen dakile jita-jita da yaɗa bayanan ƙarya.
