Kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa’kamatis Sunnah (JIBWIS) dake karamar hukumar Kankia, a Jihar Katsina, ta sanar da rufe masallacinta na Juma’a da ya shafe fiye da shekaru 40 sakamakon ruwa da ya mamaye shi.
Guda cikin jagororin kungiyar Sheikh Khalil Kasim ne ya bayyana haka a ranar Juma’a.
Ya ce a yanzu sallar Juma’a za a rinka yinta ne a Masallacin Ibn Taymiyya dake Gurara.
Ya ce, “Saboda ambaliyar da ta shafi masallacin har ruwa ya mamaye shi ba zai yiwu a rinka salla a ciki har sai an gyara.
Shugaban kungiyar Izala a yankin, Umaru Bature, ya ce wannan shawara an cimma ta ne a wani taro da suka yi tare da Malam Tasiu Umar, babban limamin masallacin da Malam Alkhamis Rabiu, shugaban kwamitin masallacin.
Bature ya bayyana cewa kwararru sun ba da shawarar a rufe masallacin duba da yadda ruwa ya lalta shi.
Ya roki dukkan musulmai da kungiyoyi da ‘yan kasuwa su taimaka ta hanyar bada gudummawa don sake gina shi.
