Jam’iyyar (ADC) ta goyi bayan matsayar kungiyar lauyoyi ta kasa NBA na cewa kotuna ba su da hurumin shiga harkokin cikin gida na jam’iyyun siyasa, kungiyar na mai cewa hakan ya tabbatar da matsayarta a rikicin shugabanci da ke gudana a cikin jam’iyyar.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran ta na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar ranar Asabar, ADC ta ce gargadin da NBA ta yi kan amfani da kotu kan son rai, ya nuna cewa ƙarar da aka shigar domin kalubalantar shugabancinta ba ta da inganci.
Jam’iyyar ADC ta ƙara da cewa wannan matsayi ya ƙarfafa ra’ayinta na cewa rikicin ba sahihin batun shari’a ba ne, illa wani yunƙuri na amfani da tsarin shari’a domin cimma muradun siyasa.
Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Lauyoyin ke nuna damuwa kan ƙaruwar da ake samu na shigar da ƙorafe-ƙorafe a kotuna kan rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyun siyasa gabanin zaɓen 2027, duk da tanade-tanaden dokar zabe ta 2022 da ke takaita irin wannan tsoma baki.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a, NBA ta gargaɗi kotuna da kada su karɓi irin waɗannan ƙorafe-ƙorafe, tana mai nuni da Sashe na 83 na dokar zaɓe, wanda ke hana tsoma bakin kotu da kuma bayar da umarnin wucin gadi a harkokin cikin gida na jam’iyyun siyasa.
