
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa; nan ba da jimawa ba, za a kawo karshen matsalar tattalin arzikin da kasar nan ke fama da shi.
Da yake jawabi, a yayin taron sabunta samar da makamashi a Najeriya, Shettima ya ce; zuciyar Shugaba Bola Tinubu na tare da ‘yan Najeriya, sannan kuma yana sane da irin radadin da suke ji.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, taron goron gayyata ne na kafa Nijeriya a matsayin cibiyar samar da makamashi tare da sabuntawa a Afirka.
sannan kuma sauyin da aka samu na makamashi Nijeriya, ya bayar da damar zuba jari na sama da dala biliyan 410, daga yanzu zuwa shekarar 2060.