Hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta Kano tayi gargaɗin daukar matakin doka akan masu shagunan dake zubar da shara barkatai, bayan ma’aikatan hukumar sun kammala aikin tsaftace kano da safe.
Shugaban hukumar Dakta Muhammad S. Khalil ne yayi gargaɗin jim kaɗan bayan kammala kare kasafin kuɗin hukumar na shekara mai kamawa.
Dakta Muhammad ya ce hukumar ta ƙaddamar da kotun tafi da gidan ka wadda zata dinga hukunta duk wanda aka samu yana zubar da shara barkatai musamman a titunan jihar da kuma saɓawa dokar tsaftar muhalli ta Kano.
Dakta khalil yace gwamnati ta sanya ma’aikatan hukumar su fiye da dubu 30 da iyalan su a tsarin Inshorar lafiya domin samun kulawa kyauta a asibitocin jihar.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Khalil na cewa, tuni hukumar su tayi hadin gwiwa da kamfanoni masu zaman kan su domin su dinga sarrafa sharar jihar ta hanyoyi da dama wadanda suka hadar da takin zamani, ledodi da robobi.
