Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci Gwamnatin Birtaniya da ta ƙarfafa gwiwar masu zuba hannun jari daga ƙasashen waje zuwa jihar, musamman a fannonin sarrafa amfanin gona da makamashi.
Gwamnan ya buƙaci hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin babban kwamishinan ƙasar Birtaniya a Najeriya, Ambasada Peter Bowles, tare da tawagarsa a Gidan Gwamnatin Kano.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta zuba jari mai yawa wajen ginawa da faɗaɗa tituna, samar da fitilun kan titi da sauran ababen more rayuwa domin sauƙaƙa harkokin kasuwanci a Kano, tare da kira ga ‘yan kasuwar Birtaniya da su yi amfani da damarmakin zuba jari da ke jihar Kano.
Tun da farko da yake jawabi, Ambasada Peter Bowles ya ce sun kawo ziyarar ne domin ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasar Birtaniya da Kano kasancewar jihar cibiyar siyasa, kasuwanci da al’adu.
Mr Bowles ya ce kafin su ƙarasa wajen gwamnan sun ziyarci cibiyar yaƙi da cututtuka, da cibiyar kula da lafiya matakin farko da masana’antar sarrafa gyada, inda suka ga ayyukan samar da guraben aiki da tallafawa manoman karkara.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito babban kwamishinan na jaddada aniyar ƙasar Birtaniya na ci gaba da haɗin gwiwa da Kano domin bunƙasa tattalin arziki da ci gaba.
